fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Gwamnatin Jihar Kwara ta gana da shugabannin addinai kan baiwa mata damar sanya hijabi a makarantu

A ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin jihar Kwara ta gana da shugabannin addinai a jihar, inda shugabannin musulmai da na kirista suka bayyana matsayinsu tare da bayar da shawarwari kan yadda za a magance bambance-bambancen da ke kan batun hijabi a makarantun da ke ba da tallafi.

Masu ruwa da tsaki na musulmin jihar, gami da kungiyoyin matasa da na mata, sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta shawo kan tsoffin masu makarantun gwamnati don baiwa dalibai mata musulmai damar sanya hijabi.

Sun ce tunda gwamnatin jihar ta dauki irin wadannan makarantu, bai kamata tsoffin masu mishan su mallaki makarantun da ke ba da tallafi a jihar ba.

Masu ruwa da tsaki sun ce barin dalibai mata musulmai su sanya hijabi zai dace da hukuncin da babbar kotun jihar ta yanke a shekarar 2016 da kuma na Kotun Daukaka Kara a shekarar 2019.

A taron na ranar Alhamis, mataimakin gwamnan, Kayode Alabi, ya yi kira ga kiristoci da musulmai da su girmama banbancin juna, su zauna lafiya da kauna, sannan su hada hannu wuri guda don ta yanda yaran masu tasowa za su ga junansu a matsayin ‘yan kasa daya.

A karshe taron, an yanke shawarar kafa kwamitin da zai magance matsalar hijabi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *