Gwamnatin jihar Legas tasha alwashin yiwa al’ummar Idumagbo magudanar ruwa da sauran mutanen dake tsiburin jihar domin maganci matsalar ambaliyar ruwa.
Kwamishinan Ruwa, Tunji Bello ne ya bayyana hakan a ranar talata, inda yace ambaliyar ruwa matsalace data addabi duniya bakidaya.
Darektan masu yin magudanar ruwa, Mahmoud Adegbite ne ya wakilci Bello wurin aiki wannan sakon yayin da al’ummar tsuburin ke zanga-zanga akan matsalar ambaliyar ruwan.