Gwamnatin jihar Legas zata baiwa malaman makarantun gwamnati kyautar guda 12 kyautar motoci a yau ranar laraba.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a wata wasikar da mataimakin shugaban sadarwa Lawal Ganiu ya rattabawa hannu a ma’aikatar ilimi.
Inda yace gwamnatin zata baiwa mutane 12 kyautar ne ciki 22 da sukayi nasara sunayensu ya fito a cikin wa’yanda za’a baiwa kyatar, kuma za’a basu ne a bainin jama’a.
Amma gwamnatin bata bayyana ranar da zata mika masu motocin ba, sai dai tace tayi hakan ne saboda jajircewar malaman da kuma karfafa masu gwiwa.