fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Gwamnatin jihar Nasarawa ta maida Almajirai 40 zuwa jihohin asali tare da hukunta alaranmomin da suka dauko su

Kusan yara Almajiri 40 ne gwamnatin jihar Nasarawa ta maida su jihohin su na asali.

 

Kwamishinar harkokin mata da ci gaban al’umma, Misis Halima Jabiru, wacce ta bayyana hakan a ranar Litinin a Lafia, babban birnin jihar, ta ce dalilan da ya sa aka tura su jihohinsu na asali ra’ayi ne na bai daya na dukkan gwamnonin arewa.

 

Ta ce manufar ita ce a dauke yaran daga kan tituna tare da hana su fuskantar hatsarin hanya, da sauran hadari.

 

Jabiru, ta yaba wa Gwamna Abdullahi Sule saboda samar da kayan aikin da ake bukata don gudanar da aikin, tana mai cewa saboda kaunar da yake yi wa yaran ne ya sa ya dauki matakin dawo da su domin haduwa da danginsu.

Ta bayyana cewa Alaranmomin, wadanda suka dauko yaran, an kai su kotu kuma an yi musu hukunci daidai da Dokar Zartarwa da gwamnan ya sanya hannu kwanan nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *