fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Gwamnatin jihar Neja ta kama tare da mayar da Almajirai 21 zuwa Kankara a jihar Katsina

Yaran da aka ce ‘yan kasa da shekara 17 ne hukumar kare hakkin yara ta jihar ta kama hanyar su ta zuwa garin Mokwa na jihar Neja.

Darakta Janar na Hukumar Kare Hakkokin Yara na Jihar Neja, Mariam Haruna Kolo, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, ta ce an kama Almajiran ne a Minna yayin da wani Malam Habibi Abdulrazaka da ke zaune a Suleja, Jihar Neja ke dauke da su a cikin wata motar bas.

Malam Abdulrazaka ya yi ikirarin cewa iyayensu ne daga jihar Katsina suka kawo su Suleja domin su samu ilimin addinin musulunci.

Karanta wannan  Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami a wani artabu da suka yi a jihar Delta, sun kashe mutane 10

Shugabar ta yi gargadin cewa ba za a yi amfani da jihar Neja wurin zubar da yaran da aka kawo daga wasu jihohin ba.

Ta kara da cewa jihar ba za ta amince da duk wani aikin barace-barace da aka dade ba a daina ba, inda ta ce yaran da suka cika sharuda kadai za a bar su su yi karatu a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.