Gwamnatin Jihar Osun ta ba da umarnin kame wata kaka mai suna Funmilayo Olalere, da ke zaune a ƙauyen Amondo, kusa da Ile-Ife, saboda zargin da yin amfanin da tsintsiya wajen dukan jikanta, wanda hakan ya zama sanadiyyar yaron yarasa idon sa.
A cewar rahotanni, jikan na zaune tare da Mama Funmilayo wacce aka fi sani da ” Iya Ibeji Olowo ”. Kwanan nan, yaro ya yiwa kamar laifi, a kokarinta na ladabtar da shi, ta yi amfani da tsintsiya ta yi wajen dukansa.
Abin baƙin ciki, karen tsintsiya ya fada cikin idanunsa, duk da haka a maimakon ta kai shi asibiti don yi masa magani, sai ta sanya masa fitsari a ido har sai da idon ya lalace.
Maƙwabta da suka damu sun tuntubi hukumomin jihar waɗanda suka binciki tsohuwar a gidanta kuma suka kama ta.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamishinan Mata, Yara da Harkokin Jama’a na jihar, Olubukola Olaboopo, ya ce za a kai wannan tsohuwa asibitin mata na Osun inda za’ayi ta yi mata gwajin tabin hankali kafin a gurfanar da ita a gaban kotu.