Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Yobe, Honarabul Abdullahi Yusuf Opera, ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Yobe ba za ta kori Almajirai daga fadin jihar ba.
Opera ya yi jawabin ne a hirar shi da ‘yan jaridu a fadar Gwamnatin jihar Yobe, inda ya bayyana cewa, jihar Yobe da Borno sune cibiyar koyar da karatun addinin Musulinci na Tsangaya.
A jawaben nasa, ya bayyana cewa, yanzu haka gwamnatin jihar Yobe ta karbi Almajirai guda 125 daga jihar Gombe, a jiya Alhamis ma An kawo Almajirai guda 52, daga jihar Nasarawa, a wani mataki na gujewa yaduwar Annobar Cutar Corona-Virus, duk an killace Almajiran a Sansanin yan Bautar kasa dake Dizigau (NYSC CAMP) da GSSS Damaturu.
Gwamnatin jihar Yobe, karkashin jagoranci Gwamna, Hon. Mai Mala Buni, ta dade da shirye-shiryen inganta tsarin koyarwar Karatun Addinin Islama a zamanance, karkashin tsarin BESDA, wannan yunkuri ya biyo bayan matakin da gwamnatin ta dauka na sanya Dokar ta baci a bangaren ilimi matakin Sakandare da Piramare.
MMB Reporters
Mai Mala Social Media Team