fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Gwamnatin Jihar Zamfara za ta dauki kwararrun ma’aikatan lafiya 515 domin inganta kiwon lafiya

Gwamnatin Zamfara ta ce za ta dauki ma’aikata 515 na asibiti a matsayin wani mataki na dinke barakar da ke damun ma’aikata a cibiyoyin kiwon lafiya na sakandare a jihar.

Dr Bashir Maru, Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Asibitin Jihar Zamfara ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Juma’a a Gusau, babban birnin jihar.

Maru ya ce Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya umurci hukumar kula da ayyukan asibitocin jihar da ta gudanar da aikin daukar ma’aikata.

Ya ce daukar ma’aikatan wani bangare ne na kudirin gwamnatin na karfafa tsarin kiwon lafiya a jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.