..duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci
Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta sanyawa ko lika takardu ko fastocin siyasa ko talla a jikin gine-ginen Gwamnati, da duk wani wuri ko gada, ko falwaya, ko jikin sandar wutar hanya ko jikin flyover, ko duk wani gini ko kayan Gwamnati,
Majiyarmu ta ruwaito hukumar birnin Kaduna KCTA zata ciccire duk wata fastar da aka lika sannan daga bisani zata soma kama duk dan siyasa, ko kamfani ko jam’iyyar da suka kama suna like-like a fadin birnin.
Ta ce a madadin haka duk mai son tallata dan takararsa ko kasuwancinsa yana iya buga littattafai, ko Billboard, ko kananan hotunan hannu, ko kalanda da dai sauran kyaututtuka da zai iya lika hotonsa ya rabawa jama’a.
A karshe Gwamnati tayi kira ga jama’a su taimaka mata wajen sa’ido da kuma alkinta kayan Gwamnati da Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta samar a jihar domin kawata birane da kyautata jin dadin jama’a don gudun kada a lalata su
Me zaku ce?