fbpx
Monday, August 8
Shadow

Gwamnatin Kano ta biya kudin tallafin karatu na Dalubai 47 ‘yan asalin jihar Kano dake karatu a kasar Sudan

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta biya kudin tallafin karatu kimanin Naira Miliyan N133m na dalibai 47 da ke karatun likitanci a Khartoum dake kasar Sudan.

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano ta biya kudadan da suka hada da na matsugunnin Daluban gami da tikitin jirgi na dawowar Daluban gida.

Ana dai sa ran dawoawar Daluban A ranar 4 ga watan Fabrairun wannan shekara ta 2021.

Hakan ya fito ne daga bakin Shugaban hukumar karbar korafe-korafe na jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado wanda gwamnatin jihar ta dorawa nauyin bincika da kuma biyan Daluban.

Leave a Reply

Your email address will not be published.