fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana wasanni

A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da dage takunkumin da ta Sanya na hana buga wasanni a jihar.

Shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, Ibrahim Galadima ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abbati Sabo , ya fitar a Kano.

Sai dai rahoton da hukumar ta fitar ta ce, An bar masu wasanni suna fita a tisaye amma babu hada sauran wasanni da zai haifar da cunkoso.

Haka zalika Galadima ya jawo hankali kan ya zama wajubi da a cigaba da kula da ka’idojin cutar Covid-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published.