fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Gwamnatin kano Zata hada hannu da kungiyoyi masu zaman kansu domin magance matsalar talauci da karancin abinci mai gina jiki

Gwamnatin kano ta ce A shirye take ta hada hannu da kungiyoyi masu zaman kansu domin magance matsalar talauci da karancin abinci mai gina jiki.

Mataimakiya ta  musamman ga gwamnan kano kan harkokin kula da lafiya, Dakta Fauziyya Buba Idris ce ta bayyana hakan a yayin bikin ranar abinci ta duniya da kungiyar bayar da tallafi ta ( Bank Charity Association of Nigeriata)  ta shirya a dakin karatun na Murtala Muhammad da ke jihar.
 
Dokta Fauziyya ta yi nuni da cewa, a lokacin da gwamnati ta sanya dokar kulle sakamakon bullar cutar COVID-19, gwamnatin jihar kano ta raba kayan abinci ga mabukata a fadin kananan hukumomin 44.
 

Tun da farko, daraktan kungiyar, Hajiya Maryam Garba Danjuma, ta ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar ne don yin biki tare da taimaka wa marasa karfi a cikin al’umma.

Inda ta kara da cewa babban abin da kungiyar ta fi mayar da hankali a kai shi ne taimakawa marasa karfi da su ka hada da basu abinci, tufafi da kuma kula da lafiya da sauransu.

Mataimakin Shugaban Jami’ar Skyline dake Kano, Farfesa Sudkar Kota da Dokta Ghazali Ado na Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano da Dokta Zaitun Mahmoud na Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Emirate suna daga cikin manyan mutanen da suka gabatar da takardu, a cewar wata sanarwa da Auwalu Musa Yola ya fitar, kakakin ofishin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay you