fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Gwamnatin Kwara ta dage jarabawar karshe na ‘yan firamare har sai abinda hali yayi

Gwamnatin jihar Kwara ta dage jarabawar kamla karatu na ‘yan firamare na shekarar 2020 da aka sake sanyaw a ranar Asabar, 24th Oktoba 2020.

Wannan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren yada labarai na ma’aikatar, Yakub K. Aliagan ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce, “An dage jarabawar Karshe ta ‘yan firamare ne, wacce aka tsara yin ta a ranar Asabar, 24 ga watan Oktoban 2020 har zuwa wani lokaci. Wannan ya faru ne sakamakon rikice-rikicen matasa wanda ke barazana ga tsaron dalibanmu da ma al’umma baki daya. 

Sanarwar ta tabbatarwa iyaye da cewa gwamnatin jihar za ta sanar da su sabuwar ranar da za a sanya da wuri-wuri.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *