fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Gwamnatin kwara ta ware Naira Miliyan N500 don tallafawa ‘yan kasuwar da aka wawushe musu kayayyakin su

Gwamnan jihar kwara Abdulrahman Abdurrazak ya ba da sanarwar samar da kudi har kimanin Naira miliyan 500 don taimaka wa masu kamfanoni da ‘yan kasuwar da aka wawure musu kayayyakin su, a wani bangare na kokarin gwamnati na dawo da ‘yan kasuwar  kan kafafunsu.
AbdulRazaq ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a garin Ilorin bayan ya duba barnar da wasu bata gari su aikata, a cewar sa bata garin sun fake ne da zanga-zangar adawa da rundunar SARS inda su ka wawashe kayayyakin jama’a.
Gwamnan ya yi Allah wadai da “wawushe dukiyar, inda ya sha al’washin taimakawa ‘yan kasuwar da su kai asara.
A karshe gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da hadin kai da rundunar ‘yan sanda domin cigaba da tabbatar da tsaro a fadin jihar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *