Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu ya kaiwa ‘yan jaridar da masu tada zaune tsaya suka kaiwa hari jiya yayin da suke dawowa daga rakiyar Tinubu.
Dan takarar jam’iyyar APC na shugaban kasa, Bola Tinubu jiya ya koma jiharsa ta Legas bayan ya lashe zaben fidda gwani na APC, wanda ‘yan jaridar suka raka shi fadar sarki Oba Riliwanu Akiolu.
Inda a hanyar dawlwarsu bata gari suka kai masu hari suka bata masu mota tare da jiwa wasu rauni a cikinsu.
Kuma yanzu gwamnan jihar Sanwo Olu ya bukaci hukuma ta gaggauta nemo mutanen da suka aikata wannan bannar don a hukunta su.