fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Gwamnatin Najeriya ta ɗau lauyoyi domin tsayawa Ekweremadu

Gwamnatin Najeriya ta yi hayan lauyoyin domin tsaywa Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai da matarsa Beatrice.

Sanata Ahmad Lawan ya shaida haka a zaman majalisa na wannan Larabar lokacin da yake sanar da cewa tawagar mambobin majalisar za su ziyarci Ekweremadu a Landan a ranar 1 ga watan Yuli.

A makon da ya gabata aka kama Ekweremadu da matarsa tare da gabatar da su a Kotu kan zargin cire kokarin cire sassan jiki wani yaro.

Ana tsare da shi yanzu haka yayinda za a cigaba da sauraren karar ta su a ranar 7 ga watan Yulin 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published.