Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin, 14 ga watan Yunin 2021 a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola wanda ya bayyana hakan, ya shawarci ‘yan ƙasar da su bai wa gwamnatin jam’iyyar APC haɗin kai “domin samar da dunƙulalliyar ƙasa kuma mai arziki”.
Ana gudanar da bikin Ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya duk ranar 12 ga watan Yuni, sai dai za a gudanar hutun ranar ne a Litinin saboda ta faɗo ranar Asabar.
Wannan ne karo na huɗu da za a gudanar da bikin a ranar 12 ga Yuni tun bayan da Shugaba Muhammdu Buhari ya sanar da sauya ranar daga 31 ga Mayu a Yunin 2018.
Ministan ya nemi ‘yan ƙasa da su guje wa duk wani abin da zai jawo wa haɗin kan ƙasa tangarɗa.