Gwamanatin tarayya ta horas da manoman rogo guda 120 daga jihar Ondo Edo da kuma Ekiti yadda zasu magance matsalar kwari a gonakinsu musamman kudajen dake lalata rogo.
Gwmantin ta bayyana cewa an samu karancin rogo daga wa’yan nan jihohin dake nomar sanadiyyar kwarin da suka mamaye masu gonaki.
Amma yanzu sunyi kira kuma gwamnati ta amsa ta wayar masu da kai akan yaddda shawo kan lamarin,
Inda ministan Noma Dr. Muhammad Abubakar ya bayyana cewa gwamnati na iya bankin kokarinta don ganin cewa ta inganta harkar noma a kasar.