fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Gwamnatin Najeriya tayi barazanar daure duk wanda ke sayar da taki sama da farashin data amince dashi N5000

Gwamnatin Tarayya ta bukaci ‘yan Najeriya da su kai rahoton duk wani da aka samu yana sayar da takin zamani sama da farashin da Gwamnatin ta amince da shi.

Shugaban Kwamitin kan takin zamani kuma gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan kokarin da gwamnati take wajan samar da taki mai araha ga manoma.

Manema labarai sun ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta rage farashin buhun taki daga dubu N5,500 zuwa dubu N5000 don tallafawa manoma, a sakamakon bullar cutar Covid-19.

Shugaban kwamnitin ya kara da cewa  Gwamnatin Tarayya ta sami labarin kokarin da wasu mutane ke yi wajen dakile kokarin da gwamnati ke yi na samar da takin zamani don wadatar da manoma a Najeriya.

“Mun samu labarin cewa wasu mutane suna siyar da takin zamani a kan N5,500 a kowanne buhu wanda hakan ya saba da farashin da gwamnati ta amince dashi.Inji shi

Ya kuma kara da cewa “A kwai  nambobi da muka sanya a kowanne buhu dan haka kuna da damar kiran mu dan kai rahotan duk wanda ya siyar da takin sama da yadda gwamnati ta amince dashi.Inji shi

A karshe ya ce Duk wanda aka kama da sai da takin, ba’a farashin da gwamnati ta amnince ba, lalle zai fuskanci hukuncin dauri a gidan yari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *