fbpx
Wednesday, February 24
Shadow

Gwamnatin Najeriya za ta sanya Kyamarar CCTV a kan manyan titunan Najeriya>>Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Dingyadi

Ministan Harkokin ‘yan sanda, Muhammad Dingyadi ya sanar da cewa gwamnatin Najeriya za ta girke kyamarorin CCTV a kan dukkan manyan hanyoyin da ke fadin kasar.
A cewarsa, wannan na daga cikin matakan dakile yawaitar satar mutane a fadin kasar.
Dingyadi, wanda yake magana a ranar Talata yayin wata hira da shi a gidan Talabijin na Channels ya ce Shugaba Buhari ya amince da aikin kuma Gwamnati ta shiga yarjejeniya da Kamfanin Fasaha na NPS don sake gyara aikin CCTV da aka yi watsi da shi.
“Muna ci gaba kamar yadda kuka sani, aikin CCTV miliyan 470 da aka yi watsi da shi. Shugaban kasar yanzu ya bamu damar sake farfado da aikin kuma tuni mun shiga yarjejeniya da kamfanin fasaha NPS. Suna can suna ƙoƙari su sake gyara duk tsarin don sake farfado da shi.
Ministan ya bayyana cewa sanya na’urar CCTV zai taimakawa Najeriya wajen magance matsalolin satar mutane a kasar.
Ya kara da cewa za a girka CCTV a dukkan manyan hanyoyin da ke fadin jihohin.
“A lokacin da aka sanya wannan tsarin CCTV, za mu samu fasahohi da yawa don kula da batun satar mutane. Za mu tabbatar mun rage yawan satar mutane a kasar nan, ”Ministan ya kara da cewa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *