Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da ceto akalla mutane 10 daga cikin mutane 21 da ‘yan bindiga suka sace a jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar Alhaji Mohammad Dani Idris, shine ya bayyana hakan a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ranar Talata, a Babban Asibitin jihar dake Minna a a yayin da likitoci ke duba lafiyar wadanda aka ceto.
Hakanan kwamishinan ya musanta rade-radin biyan fansa wajan ceto wadanda a kai garkuwa dasu inda ya shaida cewa gwamnati tabi wasu dabaru ne wajan ceto mutanan.