fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

GWAMNATIN SHUGABA BUHARI ZA TA SAMAR DA GANDUN DAJIN KIWON JAKUNA A JIHOHIN BAUCHI DA EBONYI

Cibiyar bincike don bunkasa kiwon dabbobi a Najeriya NAPRI da hadin gwiwar wasu abokan hulda za su yaki tare domin samar da gandun kiwon jakuna a jihohin Bauchi da Ebonyi.

Kamfanin dillancin labarai na kasar NAN ya ruwaito shugaban cibiyar Farfesa Abdullahi Mohammed na cewa sun kulla wata yarjejeniya da abokan huldarsu a watan Fabrairu domin samar da jakai miliyan biyu a Najeriya nan da shekara biyar zuwa 10.

 

Farfesan ya ce shirin zai iya samarwa da kasar kudin shiga da suka kai dala biliyan biyu a ko wacce shekara.

Karanta wannan  An baiwa gwamnati shawarar ta halattashan wiwi wai hakan zai sa a daina Fasa kwaurinta

 

Bayan bunkasa kiwon jakai da shirin zai yi, zai kuma taimaka wajen fadada komar tattalin arzikin kasar a bangaren kiwo da harkar noma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.