Gwamnatin tarayya tayi fashin baki akan bukatun da kungiyar malamai ta ASUU ke son a biya mata, inda tace abin nasu yayi yawa sosai.
Karamin ministan kwadago ne ya bayyana hakam wato Fetus Keyamo yayin dayake ganawa da manema labarai na Channels.
Inda yace ASUU naira triliyan 1.2 ta bukata alhalin gabdaya kudin shiga na kasa naira triliyan 6.1 ne, kuma basu kadai bane akwai ayyukan da gwamnatin ke son ta kaddamar, sannan kuma akwai ma’aita sosai hadda ma na kiwon lafiya.
Inda yace ko albshin ASUU na baya naira biliyan 412 ne wanda hakan ya kasance kashi hamsin na albashin gwamnatin tarayya bakidaya.
Saboda haka sahawarar da zai ba iyayen dalibai itace su roki kungiyar malamai ta ASUU ta janye yajin aiki yaransu su koma makaranta.