Akanta janar Anamekwe Nwabuoku ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana ciyo bashi ne don biyan albashin ma’aikatanta.
Anamekwe Nwabuoku ya bayyana hana ne ranar talata a taron da suka gudanar tare da ma’aikatan ofishinsa.
Inda yace matsalar tsaro na lunkume kudin gwamnati saboda hakan ne take ciwo ciyo bashi domin biyan bukatunta da kuma albashin ma’aikata.