Thursday, July 18
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta amince ta biya sama da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi

Gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC a wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar Litinin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin kasar, George Akume a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin sai abinda hali ya yi da kungiyoyin kwadagon suka fara a wannan rana.

Bangarorin biyu sun shafe sa’oi biyar zuwa shidda suna tattaunawa da juna kuma a karshe sun cimma matsaya a kan wasu batutuwa.

Ministan yada labaran kasar Mohammed Idris ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta amince ta yi kari a kan naira dubu 60 wanda shi ne sabon albashin mafi karanci na ma’aikata da ta gabatar wa kungiyoyin kwadagon tun farko, wanda suka yi fatali da shi.

Karanta Wannan  Kotu ta samu Donald Trump da laifukan tuhume-tuhume 34 da ake masa

Ministan ya yi ikirarin cewa a karkashin yarjejeniyar da suka cimma kungiyoyin kwadagon sun amince su janye yakin aiki:

‘’ Na farko za su janye wannan yajin aiki nasu, na biyu kuma gwamnati ta yi alkawarin za ta sake duba mafi karancin albashi da ake biyan ma’aikata, watau naira dubu 60 domin ayi mu su kari”

”Na uku za a ci gaba da tattaunawa tsakaninmu da ‘yan kwadago, kwamiti da gwamnati ta kafa zai ci gaba da tattaunawa da su na kusan sati daya, kusan kullum za su yi ta ganawa domin a samu sabon tsari na mafi karancin albashin da za a rika biyan ma’aikata” in ji shi.

Karanta Wannan  Idan har yau, Kwanaki 3 bayan shugaban kasa yayi dokar sabon taken Najeriya baka iya rerashi ba, kai me laifine kana cin amanar kasa, kuma idan aka kamaka zaka dandana kudarka>>Hukumar 'Yansanda

A dayan bangaren kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun ce za su gudanar taron Majalisar koli a ranar Talata da safe domin su tattauna kan matsayar da suka cimma da jami’an gwamnati.

Mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya Komrade Kabiru Ado Minjibir ya shaidawa BBC cewa an baiwa kwamitin da aka dorawa alhakin tsara sabon albashi mafi karanci kwanaki bakwai ya kamala tattaunawa da kungiyoyin kwadago da sauran masu ruwa da tsaki wajan tsayar da mafi karancin albashi:

”A bangarenmu mun yi alkawarin za mu kira taro na Majalisar koli wanda ya hada da wadannan kungiyoyi na NLC da TUC domin a tattauna sannan a fidda matsaya” in ji shi.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a shekara daya da ta yi tana mulki, ko me aka yi da kudin?

Game da maganar wutar lantarki kuwa, kungiyar kwadago ta NLC ta ce majalisar dokokin kasar ta ce ta yi wani kuduri da ya nemi a mayarda farashin kudin lantarki kamar yadda yake a baya

Comrade Minjibir ya ce ‘yan Majalisar dokokin kasar sun yi alkaurin za su ci gaba da bibiya domin su tabbaar cewa wannan umurni nasu, majalisar zartarwa ta yi amfani da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *