fbpx
Saturday, December 3
Shadow

Gwamnatin tarayya ta ayyana 2 da 3 ga watan Mayu a matsayin ranakun hutu domin bikin ranar ma’aikata da kuma bukukuwan Sallah

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin 2 da Talata 3 ga watan Mayu, 2022 a matsayin ranakun hutun jama’a domin gudanar da bukukuwan ranar ma’aikata da bukukuwan Sallah na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya. Ya taya ma’aikata a fadin kasar nan murnar bikin na bana, ya kuma yaba wa ma’aikata bisa kwazonsu da sadaukarwar da suke yi, inda ya ce kokarin da suke yi shi ne sanadiyar daukakar kasar da kuma martabar da Najeriya ke samu a yanzu ga kasashen duniya.

Ministan ya kuma taya daukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *