fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Gwamnatin tarayya ta ba da Umarnin tilasta Yin amfani da Takun-kumin rufe hanci a duk fadin kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci gwamnatocin jihohi da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) da su aiwatar da amfani da Takun-kumin rufe hanci a wuraren jama’a a fadin kasar.

Shugaban Kwamitin kan cutar COVID-19, Mista Boss Mustapha ne ya sanar da hakan a taron tattaunawar yau da kullun dake gudana a Abuja a ranar Alhamis.

Boss Mustapha, ya bayyana hakan ne a yayin da yake bita kan ayyukan kwamitin, ya ce shugaban ya kuma amince da saukaka dokar kulle har tsawan sati 4.

Shugaba Buhari ya kuma nemi PTF da ta hada gwiwa da jihohi da kananan hukumomi don inganta wayar da kan al’umma game da cutar.

“Ya kuma karfafa gwamnatocin jihohi da su hada hannu da hukumomin kananan hukumomi don kara daukar matakan da suka wajabta na kariya kamar su rage cunkosu, sanya takukumi, da tsaftar hannu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *