Sunday, March 29
Shadow

Gwamnatin tarayya ta baiwa ma’aikatanta hutu sai abinda hali yayi

Gwamnatin tarayya ta baiwa ma’aikatanta hutu inda tace ma’aikata da bana aiki na musamman ba daga mataki na 12 zuwa kasa su zauna a gida.

 

Sanarwar daga shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya tace ma’aikatan su ci gaba da aiki daga gida.

 

Ta kuma basu shawarar bin ka’idojin da aka gindaya dan yaki da cutar watau nesantar tarukan jama’a da kuma tsafta.

 

Tace ma’aikatan da zasu rika zuwa aiki kuma su tabbatar sun tsagaita yawan mutanen da zasu rika gani.

 

Sanarwar bata bayyana ranar dawowa aiki ba inda tace har sai abinda hali yayi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *