Gwamnatin tarayya ta bayar da ranekun litinin 25 da talata 26 ga watan Disambar sherarar 2017 da kuma litinin 1 ga watan Janairun 2018 dan yin bukuwan Kirsimeti dana sabuwarshekara, da yake sanarwa a madadin gwamnatin tarayya, ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau yayi kira ga mabiya addinin kirista da suyi amfani da wannan dama wajan yiwa Najeriya addu’ar cigaba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Haka kuma yayi kira ga ‘yan Najeriya da suci gaba da bayar da gudummuwa wajan hadin kai da zaman lafiya tsakanin al’umma, ya kuma yi kira da cewa a baiwa gwamnatin shugaba Buhari goyon baya a shirinta na inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
A karshe ya taya murnar kirsimeti da kuma sabuwar shekara.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});