Gwamnatin tarayya ta bayar da umurni cewa a kulle gabadaya makarantu masu zaman kansu saboda matsalar tsaro da kuma alwashin da ‘yan bindiga yi na cewa zasu kai masu hari.
A yau ranar laraba ne kungiyar makarantu masu zaman kansu ta bayyana hakan inda tace ta samu wasikar ne daga sakatariyar babban birnin tarayyar.
Kuma hakan ya biyo baya ne bayan gwamnatin ta rufe gabadaya makarantunta dake baban birnin tarayyar kan matsalar tsaron.
‘Yan bindigar sun sha alwashi ne cewa zasu kai hari jihar Kaduna, Abuja da kuma babban birnin tarayya kwanan nan.