Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata hukunta gidajen man dake sayar da litar man fetur a sama da kudin data kayyada masu na naira 165.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne biyo bayan wahalar man fetur da kasar ke fama da shi a babban birnin tafayya da kuma wasu jijohinta.
Shugaban hukumar man fetur ta NMDPRA, Farouk Ahmad ne ya gargadi ‘yan kasuwar ta man fetur dake sayar da man a farashin naira 180, domin yace za’ hukunta su