fbpx
Friday, January 15
Shadow

Gwamnatin tarayya ta bayyana guraren da za’a gina sabbin kwalejojin ilimin tarayya a jihohi 6

Gwamnatin taraya ta bayyana ainahin guraren da za’a gina sabbin kwalejojin Ilimi na gwamnatin tarayya 6.

 

A ranar juma’ar data gabatane dai gwamnatin ta bayyana cewa zata gina sabbin kwalejojin ilimin kimiyya a bangarori 6 na kasarnan.

 

A sanarwar data fitar, Ma’aikatar Ilimi ta gwamnatin tarayya ta hannun daraktan kula da hukdar Jama’a, Mr Ben Goong ta bayyana cewa, ta aikewa gwamnoni takardu da sanar dasu guraren da za’a gina sabbin kwalejojin ilimin.

 

Yace akwai kuma wasu rade-radin karya dake yawo a shafukan sada zumunta shiyasa suka fitar da ainahin inda za’a gina Makarantun.

 

A Jihar Bauchi yace za’a gina makarantarne a Jama’ar, sau kuma a jihar Benue za’a ginata ne a Odugbo, Karamar Hukumar Apa, sai a jihar Ebonyi za’a ginata ne a Isu, karamar hukumar Onicha, sai a jihar Edo kuma za’a ginata ne a Ekiadolor, karamar hukumar Ovia North East,  sai a jihar Osun kuma za’a ginane a Iwo, karamar hukumar Iwo, sai a Sokoto kuma za’a gina tane a Gidan Madi, dake karamar hukumar Tangaza.

 

Ya bayyana cewa za’a fara gininne a watan Octoba idan Allah ya kaimu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *