fbpx
Friday, May 27
Shadow

Gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da shuwagabannin al’umma dan magance rikicin manoma da makiyaya

Bayan daya ziyarci jihar Adamawa dan ganewa idonshi yanda rikicin fulani makiyaya da manona ya kasance, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya gana da shuwagabannin al’umma a wani sabon tsari da gwamnatin tarayya ta fito dashi dan magance rikin manoma da makiyaya da yaki ci yaki cinyewa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Sarkin Kano Muhammad Sanusi na II da lamidon Adamawa, Muhammad Barkindo da kuma uban kasa, Muhammad Barkindo, da kuma wasu shuwagabannin fulani sun halarci ganawar da shugaban kasar.

Me magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, ya bayyanawa manema labarai cewa ganawa ta gaba zata kasancene tsakanin wadanda rikice-rikicen suka shafa, kuma wakilan sun gabatarda wani rahoto akan binciken da aka gudanar kan abubuwan da suke haddasa rikicin kuma an duba su.

Haka kuma taron yayi Allah wadai da wannan rikice-rikicen musaman yanda yake shafar kananan yara da mata kuma mataimakin shugaban kasar ya tabbarwa da wakilan kokarin gwamnatin tarayya na ganin ta samar da yanayin zaman lafiya da kuma kawo karshen duk wasu rikice-rikice dake faruwa a yankuna daban-daban na kasarnan.

Bayan ziyarar da mataimakin shugaban kasar kai jihar ta Adamawa inda aka samu mummunan tashin hankali tsakanin makiyayan da manoma wanda yayi sanadiyyar rasa rayuka, an kai kayan agaji irinsu abinci da kayan amfanin yau da kullun sawa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Ni dai nasan ba zan iya ja da Atiku da Wike ba wajan wasa da kudi>>Dele Momodu

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.