fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Gwamnatin tarayya ta fasa cire tallfin man fetur

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da bayar da tallafin man fetur a kasar, matakin da ke zuwa a daidai lokacin da ‘yan kasa ke ci gaba da fargaba kan yiwuwar kara farashin mai.

A ranar Litinin ne aka fitar da sanarwa da ke tabbatar da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta jingine shirin janye tallafin man fetur bayan wani taro da aka gudanar karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan.

Mahukunta a Najeriya dai sun yi bayani kan aniyarsu ta ci gaba da ba da tallafin man fetur a wannan shekara wanda tun a farkon wannan shekara ‘yan ƙasar suka shiga fargaba, sakamakon rashin sanya tallafin man fetur a kasafin kuɗin bana.

Karanta wannan  Matsalar Tsaro: Gwamna El-Rufai zai tayar da wasu kauyuka 3 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Mai taimakawa Sanatan kan hulda da jama`a, Alhaji Bashir Hayatu Jantile, ya shaida wa BBC Hausa cewa Sanata Ahmed Lawan ya gayyaci masu ruwa da tsaki kan harkar man fetur inda ya nuna musu damuwarsa da sauran ‘yan majalisar da kuma shaida musu tattaunawar da ya yi da shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.