fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Gwamnatin tarayya ta gargadi Likitoci kan yawan mutuwar masu Coronavirus/COVID-19

Gwamnatin tarayya ta ja kunnen Likitocin Najeriya kan mutuwar masu Coronavirus/COVID-19 inda tace rashin baiwa Marasa Lafiya kukawar data kamata ya jawo ana rasa rayuka.

 

Ministan Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da Likitoci a Abuja. Yace sun samu rahoton cewa ana kin karbar marasa Lafiya saboda ba Gado sannan kuma wasu idan aka musu gwaji yana daukar lokaci kamar sati 3 kamin sakamako ya fito, yace wasu kuma masu jinyar Coronavirus/COVID-19 ana barinsu ba tare da kukawa ba.

Yace duka wadannan matsaloline dake kawo yawan mace-mace da basu kamata dan haka duk wanda aka samu matsala a Asibitinshi to shi za’a kama da laifi.

Karanta wannan  Zan iya rantsuwa da alkur'ani cewa Atiku ne ya lashe zaben shekarar 2019, cewar Buba Galadimar

 

Yace koda babu gado to a Duba mara Lafiya koda akan kujerane.

 

Ya kuma bayyana cewa an duba maganin Coronavirus da kasar Madagascar ta kawowa Najeriya inda yace binciken da aka yi ya nuna cewa abinda aka yi amfani dashi wajan hada maganin ana samunshi a Najeriya.

 

Yace kuma nan bada Jimawa ba idan aka samu kudin tallafi Najeriyar zata ci gaba da binciken Maganin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.