Saturday, April 26
Shadow

Gwamnatin tarayya ta haramtawa ‘yan mata ‘yan kasa da shekaru 18 shiga Otal

Gwamnatin tarayya karkashin Ma’aikatar mata ta haramtawa Kananan yara ‘yan kasa da shekaru 18 shiga otal.

Ministar matan, Uju Ohaneye ce ta bayyana hakan inda tace dole duka otal din dake Najeriya dolene su bi wannan umarni.

Tace duk Otal din da aka samu bai bi wannan umarni ba zai iya fuskantar hukuncin dakatarwa.

Tace an dauki matakanne dan kawar da matsalar safarar ‘yan mata.

Hakan na zuwane dai a yayin da wasu bidiyon ‘yan mata dake da shekarun tsakanin 15 zuwa 16 aka ga an yi safarar su zuwa kasar Ghana dan yin Karuwanci.

Karanta Wannan  Jihohi 22 sun kashe Naira Biliyan 251 wajan Biyan Bashi a cikin watanni 9

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *