fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Gwamnatin tarayya ta jinjinawa gwamna Wike bayan ya cika alkawarin gina babbar makarantar lauyoyi a tarihin Najeriya

Gwmnatin tarayya ta jinjinawa gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike bayan ya cika alkawarin daya yi na gina makarantar lauyoyi ta Dr. Nabo Graham Douglas Campus a Patakwal.

Inda tace tabbas Wike shugaba ne na gari domin ya kammala gina makarantar lauyoyin daya sha alwashin ginawa a jihar Patakwal, wacce ta kasance mafi girma a tarihin Najeriya.

Wike ya mika takaddun shaidar ginin makarantar a wani taro inda yasha alwashin kammala ginin makarantar kuma yace a kowane wata zai rika bayar da naira miliyan goma.

Shugaban Ilimi chief Emeka Ngige ya bayyana cewa gwamna Wike yayi alkawarin kuma ya cika tun kafin wa’adin daya saka yayi, domin a watan Yuli na bara yayi alkawarin kuma ya cika shi a watan Yuni na wannan shekarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.