Ministan Kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu ya kaddamar da wata mota da matashi dan Najeriya, Auwal Hassan ya kera.
Ministan ya bayyana motar ne a jiya, Litinin inda ya bayyana cewa, yana kira ga matasa da su rungumi bangaren Fasaha dan rika kera abubuwan da ake shigo dasu daga kasashen waje.
Ya bayyana cewa gwamnati zata hada kai da matasa dan samar da tallafi waja kere-kere.