Gwamnatin Tarayya ta kara harajin taba Sigari zuwa kaso 30 cikin 100.
Karamin ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora ne ya bayyana haka inda yace an kara harajin daga kaso 20 zuwa kaso 30 dan karfafa dena shan tabar.
Ya bayyana hakane a Abuja wajan kaddamar da wani tsari na kashe gwiwar masu shan taba sigari.