fbpx
Monday, March 1
Shadow

Gwamnatin Tarayya ta raba kayan aikin gona kyauta da iri mai inganci ga kananan manoma a jihar Gombe

Gwamnatin Tarayya ta raba kayan aikin gona kyauta da iri mai inganci ga kananan manoma a jihar Gombe, a cewar wata sanarwa da aka fitar a Abuja, ranar Lahadin data gabata daga Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara.

Sanarwar ta fito ne daga Mista Ezeaja Ikemefuna, babban jami’in yada labarai na ma’aikatar aikin gona wanda ya ambato karamin Ministan, a ma’aikatar, Mustapha Shehuri, wanda ya bayyana manufar samar da kayayyakin ga kananan manoma da cewa cigaba ne da zai bunkasa harkar Noma da samar da abinci mai gina jiki tare da samawa matasa aikin yi.

Ministan yayin gabatar da taron a harabar ofishin ma’aikatar da ke Gombe, ya ce hakan na daga cikin matakan rage radadi da cutar covid-19 ta haifar da Kuma ambaliyar da ta lalata gonaki.

Haka zalika ya sha Al”washin cigaba da tallafawa manoma domin cigaba da bunkasa ayyukan Noman Rani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *