fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Gwamnatin tarayya ta raba kayan tallafi ga Mabukata a Jihar Sokoto

Gwamnatin Tarayya ta fara raban “tan” na hatsi guda dubu 3,659.7 zuwa ga masu bukata su kimanin dubu 80,405 a Jihar Sakkwato, a wani bangare na matakan rage radadi da cutar COVID-19 ta haifar.

 

AVM Muhammadu Muhammed, Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Shine ya bayyana hakan a yayin gabatar da kayayyakin abincin ga gwamnatin jihar, A ranar Talata.

 

Muhammad wanda ya samu wakilcin Onimode Bandele, ya bayyana jerin kayyayakin da Gwamnatin ta mika ga jihar wadanda su ka hada da Tan dubu 1, 701.6 na Masara sai tan dubu 173.10 na gero da kuma tan dubu 1,785 na dawa.

Shima da yake jawabi, Gwamna Aminu Tambuwal wanda shima ya samu wakilci daga Sakataran gwamnatin jihar Sa’idu Umar ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya, ya kuma kara da cewa hakan zai taimaka sosai wajen rage radadin wahalar da mutane ke fuskanta a kasar.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *