Gwamnatin tarayya ta sanar da rage harajin da take karba akan motocin da aka shigo dasu daga kasar waje daga kaso 35 zuwa kaso 20.
Kakakin hukumar kwastam, Timi Bomodi ne ya bayyana haka bayan da jaridar The Cable ta tuntubeshi.
Ya bayyana cewa, wannan ragin zai yi amfani akan dabbi da tsaffin motocin da aka shigo dasu Najeriya daga kasashen waje.
Ya kuma bayyana cewa, Tuni suka fara aiki da wannan sabon tsari.