Sunday, May 31
Shadow

Gwamnatin tarayya ta roki ‘yan kasuwa da kada su kara farashin kayan masarufi

Gwamnatin tarayya tayi kira ga yan kasuwa dasu guji hauhawar farashin kayayyakin abinci da sufuri yayin da kasar ke gwagwarmayar shawo kan cutar Coronavirus (COVID-19) a kasar.

Alhaji Lai Mohammed, Ministan Yada Labarai, Al’adu, da yawon shakatawa ne, ya yi wannan kiran a gaban Kwamitin yaki da cutar coronavirus, a ranar Alhamis, a Abuja.

Lai Ya kara da cewa akwai bukatar nuna tausayi ga dukkan ‘yan Najeriya ta hanyar sassautawa tare da hana hauhawar farashin kayan masa rufi.

A cewar sa “Wannan lokaci ne da mutane ke bayar da tallafi don rage radadi ga al’umma. Inda ya kara da cewa “Muna kira ga ‘yan uwanmu da kar suyi amfani da wannan damar don zaluntar jama’a.

 

Idan zaku iya tunawa a makwannin baya gwamnatin Jihar kano ta zauna da ‘yan kasuwar jihar don cimma matsaya kan sassauta farsashin kayayya kin abinci, wanda daga bisanine gwamnatin da kuma ‘yan kasuwa suka amince da farashin da gwamnatin jihar ta cimma matsaya akai.

Haka zalika itama jihar Bauchi ta dauki mataki makamancin wannnan inda gwamnan jihar ya bukaci sassauta farashin kayan masarufi wanda shima daga bisanine aka cimma matsayar sassauta farashin a jihar.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *