fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Fitar Da Naira Milyan 620 Don Yaki Da Cutar Coronavirus>>Ministar Kudi

Gwamnatin tarayya ta saki naira milyan 620, kashi na biyu a kudaden da aka bayar don magance yaduwar corona virus.

 

Ministar Kudi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmad ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun mai taimaka mata, kamar yadda Leadership ta rawaito.

 

Ministar ta ce sakin kudaden da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar sun samu ne bisa ga matakin gaggawa don ganin an magance yaduwar cutar a fadin kasar nan.

 

Tace amincewar da Buhari ya yi game da sakin kudaden don magance CObID-19 ya kasance na gaggawa.

Karanta wannan  APC ta shigar da karan Tinubu a kotu cewa ta hana shi tsayawa takarar shugaban kasa

 

Ta ce “mun fitar da kason farko na naira milyan 364 a baya, yau kuma za a saki kaso na biyu milyan 620 wanda ya kawo jimlar kudin zuwa naira milyan 984”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.