Gwammatin tarayya ta kaddamar da wani sabon tallafi ga matasa a bangaren kirkire-kirkire da fasaha na dala Miliyan 618.
Mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo ne ya kaddamar da wannan tsari.
Yayi kira ga gwamnatocin Farika da kamfanoni masu zaman kansu da su talkafawa irin wadannan tsare-tsare.
Kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande yace wannan tsari zai tallafawa matasa dake tsakanin shekaru 15 zuwa 35.