Sunday, May 31
Shadow

Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 50 domin farfado da masana’antun

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ware Naira biliyan 50 domin farfado da masana’antun kasar, bayan da suka samu koma baya sakamakon annobar cutar coronavirus.

 

Najeriya kasa ce mai cike da dumbin arzikin kasa. Sai dai annobar coronavirus da ta mamaye duniya ta shafi wannan fanni, wanda hakan ya tilastawa gwamnati daukar matakin da ya dace. Gwamnatin dai ta shirya domin bayar da tallafi da ya kama daga kan Naira miliyan uku zuwa 25 ga masana’antun kasar. Shi kuwa darakta janar na kungiyar masu masana’antu na kasar Mr Ambrose Uche ya koka ne kan yadda ake samun karin kudin ruwa a bankunan kasuwancin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *