Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa har yanzu tana bayar da tallafi cikin harkar man fetur, kuma bata san ana wahalar man a kasar ba.
Karamin ministan man fetur, Sylva Timipre ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a yau a babban birnin tarayya Abuja.
Inda yace gwamnatin tarayya bata da masaniya akan kara fashin litar man sai dai idan ‘yan kasuwa ne suka kara farashin.
Inda yace zasu tattauna dasu domin a shawo kan wannan matsalar.
Gwamnatin tarayya ta bayar da umurni ne a riga sayar da litar man akan naira 165 amma har sama da 200 wasu gidajen mai suna sayar da man nasu.