Hadimin shugaban kasa Muhammadu Bihari, Garba Shehu ya bayyana cewa jami’o’in Najeriya sunfi na kasar waje kyau.
Inda yace ya kamata iyaye su rika barin yaransu suna cigaba da karatunsu a Najeriya bayan sun kammala sakandiri a Najeriya su daina fita dasu kasashen waje.
Ya bayyana hakan ne a babban birnin tarayya yayin da makarantar Glisten International Academy ke bikin yaye dalibai a ranar asabar, kuma hadda yaron shi a cikin daliban.
Inda kuma yace kwanan nan gwamnatin tarayyar zata magance yajin aikin ASUU inda ya nemi iyayen dalibai dasu taya gwamnatin tarayya rokon kungiyar malaman ta janye yajin aikin da suke yi.