Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matsalar tsaro bata shafi harkar noma sosai ba a kasar Najeriya.
Ministan noma Abubakar Muhammad ne ya bayyan hakan a taron mako-mako da suke gudanarwa a fadar shugaban kasa a babban birnin tarayya.
Inda yace Najeriya itace kasa ta farko da tafi kowace kasa nomar shinka a nahiyar Afrika, sannan kuma itace ta hudu a Duniya bakidaya.
Ya kara da cewa tabbas matsalar tsaro ta shafi harkar noma musamman a arewacin Najeriya, amma ba sosai ba kuma har yanzu ana noma a Najeriya.