fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Gwamnatin tarayya tayi burus da sukar da ake yi mata, tace sai ta kara haraji akan kiran waya da sayen data

Gwamnatin tarayya tayi burus da sukar da ake yi mata kan harajin da tace zata kara akan kiran waya da sayen data da kuma tura sakonni.

Kashi biyar ne gwamnatin tarayyar tace zata kara akan kashi 7.5 da ake biya na harajin, inda gwamnatin tace hakan zai matukar habbaka tattalin arzikin kasar nan.

Mai magana da yawun Zainab Muhammad wato ministar Kudi, Tanko Yunusa ne ya bayyana hakan.

Inda yace gwamnatin ta sake jaddada wannan batun nata ne a taron data gudanar da shuwagabannin kamfanunuwan sada zumunta.

Karanta wannan  Me ke shirin faruwane: Kalli yanda ganawar Kwankwaso da Ganduje ta kasance

Kuma ya kara da cewa dama can tun shekarar a 2020 gwamnatin tayi wannan tsarin kawai bata kaddamar dashi bane akan lokaci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.